Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-01 22:04:17    
Ya kamata a share fage a dukkan fannoni, don ba da tabbaci ga shirya wasannin Olympics cikin nasara

cri
Kwanan baya, mataimakin firayin ministan kasar Sin Li Keqiang ya jaddada cewa, yanzu ana shiga wani muhimmin mataki wajen share fagen wasannin Olympics, ya bukaci hukumomin da abin ya shafa da su yi ayyuka a fannonin kiyaye muhalli, da asibiti da kiwon lafiya, da ingancin abinci, da samar da makamashi, da dai sauransu, don tabbatar da shirya wasannin Olympics cikin nasara.

A lokacin da yake bincike kan halin gudanarwa a filaye da dakunan wasannin Olympics, da kauyen wasannin Olympics a nan birnin Beijing, Mr. Li Keqiang ya nuna cewa, muhallin halittu mai kyau shi ne sharadi na farko wajen shirya wasannin Olympics cikin nasara, Beijing ta riga ta dauki matakai masu amfani kan wannan, amma za a cigaba da ayyukan kyautatta muhalli, da dai sauransu, don tabbatar da ingancin yanayi bisa daidaitaccen matsayi, bugu da kari kuma, ya kamata a gudanar da tsarin bincike kan ingancin abinci sosai, don ba da tabbaci kan lafiyar masu halartar wasannin, kazalika a yi amfani da gine-ginen tsimin makamshi daban daban, da tsayawa kan shirya wasannin Olympics ta hanyar tsimin albarkatu, da kuma neman dauwamammen cigaba.

Bayan haka kuma, Mr. Li Keqiang ya nuna cewa, a matakin karshe na share fagen wasannin Olympics, ya kamata a shirya ayyukan ba da tabbaci daban daban, don tabbatar da shirya wasannin Olympics, da na nakasassu cikin nasara. (Bilkisu)