Yau a nan birnin Beijing, shugaban kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa ya sake nuna yabo kan yadda Beijing ke share fagen wasannin Olympics, kuma yana sa rai kan samun cikakkiyar nasara a gun wasannin Olympics na Beijing.
Kafin wannan, sau da dama ne Mr.Rogge ya bayyana gamsuwarsa dangane da yadda Beijing ke share fagen wasannin Olympics. Yau yayin da yake hira da wakilinmu, ya sake bayyana irin wannan ra'ayi, ya ce, "filayen wasa suna da kyau kwarai, kuma kwamitin wasannin Olympics na Beijing ya kware sosai wajen share fagen wasannin, sabo da haka, ina sa rai kan samun nasara a gun wasannin Olympics na Beijing."(Lubabatu)
|