|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2008-08-01 20:48:51
|
 |
Ayyukan tsaro 7 na rundunar soja ta kasar Sin a lokacin wasannin Olympics
cri
A ranar 1 ga wata da safe, ma'aikatar tsaron kasar Sin, da cibiyar watsa labaru ta duniya ta birnin Beijing sun shirya taron manema labaru na hadin gwiwa, inda shugaban sashen kula da ayyukan rundunar soja na cibiyar ba da jagoranci kan aikin tsaro a lokacin wasannin Olympics na Beijing, babbar kanar Tian Yixiang ya bayyana ayyukan tsaro 7 na rundunar soja ta kasar Sin a lokacin wasannin Olympics.
A lokacin da yake amsa tambayoyin manema labaru, ya nuna cewa, ayyukan tsaro na rundunar soja ta kasar Sin a lokacin wasannin Olympics sun hada da: kula da aikin tsaro na sama, da kayyaden zirga-zigar jiragen sama a yankunan wasannin da ke birnin Beijing, da na sauran birane, da kula da tsaron wuraren da ke kewayen yankunan wasanni da ke tekuna, da kuma taimakawa hukumomin tsaron zaman lafiyar jama'a wajen yaki da lamarin ta'addanci, da nuna goyon baya wajen ba da rahoton asiri, da dai sauransu.
Bayan haka kuma, babban kanar Tian Yixiang ya gabatar da cewa, sojojin kasar Sin kusan dubu 34 daga rundunonin sojoji na teku, da na kasa, da na sama za su shiga ayyukan tsaro a lokacin wasannin kai tsaye, kuma za su ba da tabbaci sosai wajen shirya wasannin Olympics kamar yadda ya kamata. (Bilkisu)
|
|
|