Ran 1 ga wata a nan birnin Beijing, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya gana da manema labaru na kafofin watsa labaru na kasashen waje da ke kasar Sin, ya ce, ana son jama'ar kasa da kasa za su jin farin cikin tare saboda wasannin Olympics na Beijing.
Mr. Hu Jintao yana ganin cewa, inda ana son cimma nasarar gudanar da wasannin Olympics, abu mafi muhimmanci shi ne bunkasa ainihin wasannin Olympics na amincewar abokantaka, da hadin kai, da zaman lafiya. Kuma ya kamata a samr da wani dandalin gasa cikin adalci ga 'yan wasa na kasa da kasa, ta haka za su iya yin gasa yadda ya kamata. Kuma muna son abokai daga duk duniya za su kara fahimtar juna da sada zumunci ta hanyar wasannin Olympics.
Mr. Hu Jintao ya ce, gwamnatin kasar Sin tana mai da hankali sosai kan wasannin Olympics na Beijing daga fannoni 3, wato kiyaye muhallin halittu, da neman cigaba da kirkira ta hanyar kimiyya, da ilmi da al'adun jama'a.
|