Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-01 16:57:38    
Sakon shugaban Hu Jintao ga wata makarantar kasar Amirka

cri
A kwanakin baya, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya rubutu wata wasika zuwa ga kungiyar makada da mawaka ta makarantar Londonerry ta kasar Amirka don yi mata godiya bias ga nuna jajantawa ga mutane masu fama da bala'in girgizar kasa a lardin Sichuan kuma ta ba da taimako ga yara na yankin nan.

A cikin wasikar, Mr. Hu Jintao ya bayyana cewa, za a fara gasar wasannin Olympic a karo na 29 a birnin Beijing. Jama'ar kasar Sin suna fatan taken "duniya daya kuma buri daya" zai zama burin duk jama'ar duniya. Bugu da kari, yana fatan samari na kasashen Sin da Amirka za su kara mu'amala, da yin koyi da juna , da kuma kara zumunci don ciyar da dangantakar abokantaka a tsakanin kasashen biyu gaba da ba da taimako ga samun kyakyawar makomar duniya.(Asabe)