Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-01 16:55:38    
'Yan wasa fiye da dubu 10 sun tabbatar da halartar gasar wasannin Olympic ta Beijing

cri

Ran 1 ga wata, jami'in kwamitin share fagen gasar wasannin Olympic na Beijing ya fayyace cewa, an kusan kawo karshen ayyuka iri-iri na share fagen gasar wasannin Olympic ta Beijing. Kawo yanzu dai akwai 'yan wasa 11028 da suka sami iznin halartar gasar.

Ran nan, a gun taron manema labaru da babbar cibiyar kafofin watsa labaru ta gasar wasannin Olympic ta Beijing ta kira, Mr, Zhang Jilong ya bayyana cewa, kwamitin shirya gasar wasannin Olympic na kasar Sin ya riga ya ba da tabbacin ba da iznin halartar gasar wasannin Olympic na 'yan wasa 11028 ga kwamitocin wasannin Olympic na kasashe da yankuna guda 151.

Zhang Jilong ya furta cewa, tun daga ran 6 zuwa ran 24 ga watan Agusta, wato a cikin gasanni na tsawon ranaki 19, gaba daya za a gudanar da gasanni 2173 na wasannin Olymoic na Beijing, inda za a samar da lanbobin zinariya na kananan ayyukan wasa 302. Kuma an riga an tsara jadawalin gasannin.(Fatima)