A ran 1 ga watan Agusta, an fara mika wutar wasannin Olympic na Beijing a sabon garin Binhai na birnin Tianjin dake a arewacin kasar Sin, kuma an fara bikin mika wutar wasannin Olympic da za a yi a cikin kwanaki biyu masu zuwa a birnin Tianjin.
Da karfe 8 na safe, an yi bikin fara mika wutar a filin tashar ruwa ta Tianjin. Dan kwadagon mai ba da misalign koyo na kasar Sin Kong Xiangrui ya zama mai mika wuta na farko. Duk tsawon hanyar da aka mika wuta a kai zai kai kilomita 16, kuma tsawon hanyar da masu mika wuta za su mika wuta ya kai kilomita 10, ban da wannan kuma, tsawon hanyar da motoci masu nuna wutar wasannin Olympic suka bi ya kai kilomita 6. Masu mika wutar 191 za su shiga wannan aiki.(Asabe)
|