Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-31 21:09:20    
Kasar Sin ba za ta rufe kofa ga kafofin watsa labaru na kasashen waje ba bayan wasannin Olympics

cri
Kwanan baya, a lokacin da shugaban babbar hukuma mai kula da madaba'a da watsa labarai ta kasar Sin Mr. Liu Binjie ke zantawa da manema labaru, ya bayyana cewa, bude kofa ga kafofin watsa labaru ba manufar da kasar Sin ke dauka a gajeren lokaci ba, amma a cikin dogon lokaci ne. Ya ce, kasar Sin ba za ta rufe kofa ga kafofin watsa labaru na waje ba bayan wasannin Olympics.

Mr. Liu Binjie ya tabbatar da cewa, za a dakatar da gudanar da tsarin da aka tsara game da ziyarar da manema labaru na kasashen waje za su yi a nan kasar Sin a lokacin wasannin Olympics da na share fage a watan Oktoba, amma wannan ba ya nuna cewa, za a soke manufar bude kofa ga kafofin watsa labaru na kasashen waje ba, sai dai za a kara bude kofa, kuma a fili kan tsarin gudanarwa wajen watsa labarai. (Bilkisu)