|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2008-07-31 21:07:56
|
 |
Ana da niyyar ba da tabbaci wajen ingancin abinci da za a samar a lokacin wasannin Olympics a nan birnin Beijing
cri
A ranar 31 ga wata a nan birnin Beijing, kakakin watsa labarai na ofishin kula da ingancin abinci na birnin Beijing madam Tang Yunhua ta bayyana cewa, Beijing na da karfi da niyyar tabbatar da ingancin abinci da za a samar a lokacin wasannin Olympics.
Madam Tang Yunhua ta gabatar da cewa, an kafa hukumomin musamman don tabbatar da ingancin abinci a lokacin wasannin Olympics a nan birnin Beijing, a waje daya kuma, bangarori daban daban da abin ya shafa za su tafi sansanonin samar da abinci, da kamfanonin gyara abinci, da cibiyoyin jigilar kayayyaki na wasannin Olympics, don sa ido kan hakikanin ayyuka.
Bayan haka kuma, an gudanar da shirin ba da tabbaci kan ingancin abinci da za a samar a wasannin Olympics a nan birnin Beijing, wato an kafa tsare-tsare a wuraren cin abinci na jama'a, ciki har da dakuna da filayen wasannin Olympics, da hotel-hotel da aka sa hannu, da dai sauransu. (Bilkisu)
|
|
|