Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-31 20:16:39    
Kasar Sudan tana adawa da sanya siyasa cikin gasar wasannin Olympics

cri

Manzon musamman na shugaban kasar Sudan Mr. Awad ya bayyana a 'yan kwanakin baya a birnin Beijing cewa, kasar Sudan tana adawa da sanya siyasa cikin gasar wasannin Olympics, tana yaba wa aikin share fage da kasar Sin take yi wajen shirya gasar wasannin Olympics ta Beijing, haka kuma ta sanya ran alheri ga birnin Beijing da ya shirya gasar wasannin Olympics cikin nasara.

Kungiyar masu yin bincike da aka tura a karo na farko ta tawagar wakilai ta gasar wasannin Olympics ta kasar Sudan ta riga ta iso birnin Beijing, a wannan karo kuma, kasar Sudan za ta turo 'yan wasan guje guje da tsalle tsalle 8 da su shiga gasar wasannin Olympics ta Beijing, wannan ya zama tawagar 'yan wasan guje guje da tsalle tsalle na Sudan da ta fi girma bisa mataki a tarihi.(Danladi)