Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-31 16:13:30    
Shugaban Madagascar zai halarci bikin bude gasar wasannin Olympic ta Beijing

cri
Ran 30 ga wata, yayin da jami'in da ke kula da harkokin motsa jiki na kasar Madagascar yake zantawa da manema labaru na kasar Sin, ya bayyana cewa, ran 6 ga watan Agusta, Mr. Marc Ravalomanana, shugaban kasar Madagascar zai tashi zuwa birnin Beijing domin halartar bikin bude gasar wasannin Olympic ta Beijing da za a yi a ran 8 ga watan Agusta.

Jami'in nan ya bayyana cewa, makasudin zuwan shugaban Marc Ravalomanana shi ne ganin lokacin tarihi mai girma na bude gasar wasannin Olympic, yayin da yake sa kaimi ga 'yan wasan Madagascar.

Bisa labarin da aka bayar, an ce, bayan zaben da aka yi har na tsawon kimanin shekarar 1, kasar Madagascar ta riga ta tabbatar da 'yan wasa 7 da za su halarci gasar wasannin Olympic ta Beijing da gasar wasannin Olympic ta nakasassu, kuma za su halarci ayyukan wasan guje-guje da tsalle-tsalle da na iyo da na dambe da dai sauransu.(Fatima)