Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-31 16:13:13    
Manema labaru na kasashen waje za su iya ba da labarun wasannin Olympics ta hanyar Internet yadda ya kamata

cri
Ran 31 ga wata a nan birnin Beijing, Mr. Sun Weide wani jami'in kwamitin shirya wasannin Olymipics na Beijing ya ce, yayin da ake gudanar da wasannin Olympics, kasar Sin za ta gabatar da aikin hidima wajen shiga Internet ga manema labaru na kasashen waje, hanyoyin Internet na ba da labaran wasannin Olympics da labaran kasar Sin ba su da shinge.

Mr. Sun Weide ya yi nuni da cewa, kamar halayen da ake ciki a sauran kasashe, kasar Sin tana daidaita Internet bisa doka. Bisa dokokin kasar Sin, ba a iya samar da sigina masu keta doka, misalin kada a yada labarai game da kungiyar masu zuga mutane yin laifuffuka wato kungiyar Falungong da abubuwan da ke lallata moriyar kasa, kuma yana fatan kafofin watsa labaru su kiyaye dokokin kasar Sin.