
A ran 31 ga wata, an kammala aikin mika wutar gasar wasannin Olympic na Beijing a babban birnin masana'antu na arewancin kasar Sin, wato birnin Tangshan na lardin Hebei cikin nasara.

An fara mika wutar gasar wasannin Olympic a birnin Tangshan a ran nan da karfe 8 da minti 10 na safe.

Mutane masu mika wutar da yawansu ya kai 208 sun mika wutar daga hannu zuwa hannu, a karshe dai kuma, wutar gasar wasannin Olympic ta kai zangon karshe a karfe 12 da minti 17 na rana.

Ya zuwa yanzu, an kammala aikin mika wutar gasar wasannin Olympic na Beijing a lardin Hebei cikin nasara. A ran 1 ga watan Agusta, za a ci gaba da mika wutar a birnin Tian, wato birnin da ya bada hadin kai wajen shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing, wanda kuma ya kasance daya daga cikin rassan filayen wasan kwallon kafa na gaggarumar gasar. (Zubairu)
|