Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-31 14:03:10    
'Yan wasan Iraki 5 sun sami iznin shiga gasar wasannin Olympic ta Beijing

cri

Ran 30 ga wata, jami'in kwamitin gasar wasannin Olympic na kasar Iraki ya bayyana cewa, bayan soke doka hana halartar gasa ga kasar Iraki, kwamitin gasar wasannin Olympic na duniya ya riga ya gamsu da 'yan wasan Iraki 5 su halarci gasar wasannin Olympic ta Beijing ta 2008.

Ran nan Mr. Hussein al-Amidi, babban sakataren kwamitin gasar wasannin Olympic na kasar Iraki ya bayyana cewa, 'yan wasa 5 na kasar Iraki da za su halarci gasar wasannin Olympic ta Beijing sun hada da Haidar Nasir, dan wasan jefa faifan karfe, da Dana Hussein, yar wasan gudun gajeren zango, da Haidar Nozad da Hamza Hussein, 'yan wasan tseren kwale-kwale, da Ali Adnan, dan wasan harba kibiya.(Fatima)