Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-31 11:05:58    
Gidan talibijin CCTV ya tsai da shirin tinkarar matsaloli cikin gaggawa domin tabbatar da aikin watsa shirye-shiryen wasannin Olympics

cri

Gidan talibijin CCTV na kasar Sin ya tsai da shirin tinkarar matsaloli cikin gaggawa na matakai huku kan ko wane fanni domin tabbatar da aikin watsa shirye-shiryen wasannin Olympics.

Mr. Ding Wenhua babban injiniya na CCTV ya fayyace haka yayin da yake ganawa da manema labaru a nan birnin Beijing. Mr. Ding Wenhua ya bayyana cewa, shriin tinkarar matsaloli cikin gaggawa ya kunshi da matakai hudu, da farko shi ne yayin da ake yin bikin budewa, za a yi amfani da sigina ta hanyoyi biyu, wato kamfannin watsa shirye shiryen kai tsaye na wasannin Olympics na Beijing da tsarin CCTV, na biyu, dauki matakai a cibiyar rediyon duniya domin zabi sigina. Na uku, a sa'i daya kuma za a aika da sigina zuwa sabon ginin tashar CCTV da tsohon ginin tashar CCTV, na hudu, a tsohon ginin tashar CCTV, za a watsa shirye-shirye ta hanyoyi biyu.

Mr. Ding Wenhua ya nuna cewa, tashar CCTV ta riga ta shirya sosai wajen samun sigina da hanyoyin sadarwa, tana da imani sosai wajen tabbatar da aikin watsa shirye-shiryen wasannin Olympics.