Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-31 09:24:09    
Gasar wasannin Olympic ta Beijing za ta zama dandalin wasannin rarraba buri na matasan duniya, a cewar shugaban kwamitin gasar wasannin Olympic na Kango(Kingshasa)

cri
Ran 30 ga wata a birnin Kinshasa, yayin da Mr. Raymond Ibata, shugaban kwamitin gasar wasannin Olympic na Kango(Kinshasa) yake zantawa da manema labaru, ya bayyana cewa, gasar wasannin Olympic ta Beijing za ta zama dandalin wasanni na taruwar matasan duniya da na rarraba buri da kuzarinsu.

Mr. Raymond Ibata ya nuna adawa ga wasu labarun da wasu kafofin watsa labaru na kasashen yammacin duniya suka bayar wajen yin amfani da harkokin siyasa domin yin shishigi cikin gasar wasannin Olympic ta Beijing. Ya yi tsammani cewa, makasudin yada labarun shi ne domin cin zarafin kasar Sin. Ya nuna cewa, jama'ar Kango(Kinshasa) su nuna goyon bayansu sosai ga kokarin da jama'ar Sin suka yi domin cimma nasarar gasar wasannin Olympic.

Mr. Raymond Ibata ya furta cewa, ko da yake kasar Kango(Kinshasa) ta kawo karshen yake-yake, amma karfin da take da shi karami ne, amma kasar Kango(Kinshasa) ta dora niyyar cewa za ta tura tawagar da ke kunshe da mutane 29, ciki da akwai 'yan wasa da masu horaswa da kuma jami'an motsa jiki domin halartar ayyuka 4 na gasar wasannin Olympic, wato wasan guje-guje da na jido da na dambe da na iyo. (Fatima)