Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-30 19:57:52    
Ingancin iska ya samu kyautatuwa sosai a nan birnin Beijing kafin wasannin Olympics, a cewar kwarare

cri
A ranar 30 ga wata, shugaban kungiyar kula da fasahohin tabbatar da ingancin iska ta wasannin Olympics na Beijing, kuma shehun malami daga jami'ar Beijing Mr. Zhu Tong ya bayyana a gun taron manema labaru da aka shirya a wannan rana a nan birnin Beijing cewa, tun bayan da aka dauki matakin saukaka zirga-zirgar motoci a ranar 1 ga watan Yuli a birnin Beijing, an samu kyautatuwa sosai wajen ingancin iska a birnin.

Mr. Zhu Tong ya ce, bisa kididdigar da aka yi an nuna cewa, tun daga ranar 1 zuwa ranar 29 ga wata a birnin Beijing, yawan nitrogen dioxide da ke iska ya ragu da kashi 48 cikin dari, yawan carbon monoxide kuma ya ragu da kashi 42 cikin dari. Bayan haka kuma, yawan kura da jama'a suke shaka da ke cikin iska shi ma ya ragu sosai. Saboda haka, ingancin iska na birnin Beijing na dacewa da sharadin shirya wasannin Olympics. (Bilkisu)