Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-30 16:52:38    
Gwamnatin kasar Sin ta dauki matakan yaki da yin amfani da maganin sa kuzari

cri
A ran 30 ga wata, Mr. Jiang Zhixue, direktan kula da harkokin kimiyya da ilmi a babbar hukumar motsa jiki ta kasar Sin ta bayyana a nan birnin Beijing cewa, gwamnatin kasar Sin ta dauki jerin matakai wajen yaki da yin amfani da magungunan sa kuzari domin samar da wani kyakkyawan muhallin da 'yan wasannin motsa jiki na kasashen duniya za su iya yin gasa cikin adalci a gun gasar Olympic ta Beijing.

A gun wani taron manema labaru da aka yi a wannan rana, Mr. Jiang Zhixue ya bayyana cewa, babbar hukumar motsa jiki ta kasar Sin ta kulla yarjejeniya da kananan hukumomin motsa jiki na matakai daban daban domin yaki da yin amfani da magungunan sa kuzari tare, kuma ta kafa cibiyar fama da yin amfani da magungunan sa kuzari da bayar da dabarun yanke hukunci kan wadanda suke shan maganin sa kuzari da kara karfin yin bincike kan 'yan wasa. (Sanusi Chen)