Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-30 16:34:46    
Ana tabbatar da ingancin abinci domin gasar Olympic ta Beijing

cri
A ran 30 ga wata, madam Liu Yaqing, mataimakiyar shugaban hukumar aikin gona ta birnin Beijing ta bayyana cewa, za a iya tabbatar da yawan amfanin gona da ingancinsu domin gasar Olympic ta Beijing. Sabo da haka, za a iya tabbatar da samar da isashen amfanin gona ga gasar Olympic.

Madam Liu ta fadi haka ne a gun taron manema labaru da hukumar aikin gona ta birnin Beijing ta shirya.

Madam Liu ta kara da cewa, gwamnatin kasar Sin ta dora nauyin tabbatar da ingancin amfanin gona domin tabbatar da ingancin amfanin gona da za a samar wa gasar Olympic ta Beijing. Kuma ta kara ba da jagoranci da sa ido kan aikin tabbatar da inganci, har ma ta ba da taimako wajen kyautata aikin shigar da amfanin gona a kasuwa.

Madam Liu ta bayyana cewa, samar da amfanin gona mai inganci ga gasar Olympic ta Beijing wani muhimmin aiki ne. Dole ne a kara karfin yin bincike da sa ido kan ingancin amfanin gona domin cimma burin tabbatar da ganin 'yan wasa da baki sun ji dadi, kuma sun kwantar da hankulansu kan abincinmu. (Sanusi Chen)