A lokacin da ya gana da manema labarun gidan radiyon kasar Sin a ran 30 ga wata a birnin Beijing, shahararenmamban kwamitin gasar wasannin Olympic na duniya, kuma mamban kwamitin daidaituwa na gasar wasannin Olympic ta Beijing Richard Kevan Gosper ya bayyana cewa, bayan shekaru 7 na shirya gasar wasannin Olympic, za a kaddamar da gasar nan, kuma ya yi zumudi sosai a kan wannan.
A matsayin shugaban kwamitin watsa labaru na gasar wasannin Olympic ta duniya, Mr. Gosper ya nuna cewa, ingancin iska, saurin aikin internet da sauran batutuwa sun jawo hankulan kafofin watsa labaru a kwanakin nan. Yanzu ana binciken saurin aikin internet. A game da ingancin iska, Mr. Gosper ya ce, ba za a gama watsa labaru kafin a gama gasar wasannin Olympic ba, amma kwamitin gasar wasannin Olympic na Beijing ya riga ya dauki matakai. Zai ci gaba da rage yawan motoci a kan hanyar mota, rage ayyukan gurbata muhalli a masana'antu don warware batun ingancin iska. Ba dole ne a dauki wadannan matakai, amma a riga a shirya.(Asabe)
|