Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-30 14:03:07    
Nune-nune mai suna "Afrika da gasar wasannin Olympic" na Beijing

cri
Don maraba da gasar wasannin Olympic a karo na 29 da za a yi a birnin Beijing, da kuma kara mu'ammala a tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, daga ran 29 ga watan Yuli zuwa ran 3 ga watan Agusta a dakin karatu na hedkwatar kasar Sin na Beijing, ma'aikatar al'adu ta kasar Sin , gwamnatin birnin Beijing da babbar hukumar kula da watsa labaru da sinima za su yi nune-nune mai suna "Afrika da gasar wasannin Olympic".

A gun nune-nunen, za a nuna hotuna masu daraja sosai da yawa da suka bayyana alfahari da tarihin wasannin motsa jiki na kasashen Afrika da zumuncin a tsakanin jama'ar kasashen Afrika da ta kasar Sin.

A gun bikin kaddamar da nune-nunen da aka yi a ran 29 ga watan, masu yin nune-nunen sun ba da jawabi cewa, Afrika tana da tsawon tarihin wasannin motsa jiki, jama'ar kasashen Afrika suna da halin kuzari da karfin rayuwa sosai. Bayan kasashen Afrika sun shiga babban iyalin wasannin Olympic, wasanni na Afrika ya bunkasa sosai. A iya yin imani da cewa, 'yan wasa na kasashen Afrika za su ba mutane mamaki a gun gasar wasannin Olympic ta Beijing.(Asabe)