A ran 30 ga wata, an fara mika wutar gasar wasannin Olympics ta Beijing a birnin Qinghuangdao a lardin Hebei, wanda birni ne da ke hadin kan gasar wasannin Olympics ta Beijing kuma wani filin wasa ne na kwallon kafa a gasar.
A wannan rana da karfi 8 na safe, an yi bikin fara mika wutar a birnin Qinghuangdao daga yankin shakatawa na Laolongtou na Shanhaiguan, wanda ake kiran ta wurin shiga teku na babbar ganuwa. Tsawon hanyar mika wutar a Qinghuangdao ya kai kilomita 7, kuma masu mika wutar su 208 za su shiga aikin mika wutar a Qinghuangdao.(Zainab)
|