Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-30 11:16:31    
An nemi a tabbatar da ingancin muhalli a lokacin gasar Olympic ta Beijing

cri

A ran 29 ga wata a nan birnin Beijing, Mr. Wu Xiaoqing, mataimakin ministan kiyaye muhalli na kasar Sin ya bayyana cewa, dole ne yankuna da hukumomi daban daban su kara karfin sa ido kan ingancin muhalli, kuma su yi kokarin daukar matakan fama da yanayi mai tsanani sosai, kuma su sanar da ingancin muhalli daga dukkan fannoni a lokacin gasar Olympic domin tabbatar da ingancin muhalli a lokacin gasar.

Wu Xiaoqing ya kuma bayyana cewa, dole ne dukkan hukumomin da abin ya shafa su aiwatar da shirin sa ido kan ingancin muhalli da shirin fama da yanayi mai tsanani da mai yiyuwa ne zai auku cikin gaggawa. Kuma a tabbatar da matakai da ajandar daidaita matsalolin da mai yiyuwa ne za su auku cikin gaggawa. Haka kuma su kafa tsarin fama da matsalolin da suke faruwa cikin gaggawa. Bugu da kari kuma, Mr. Wu Xiaoqing ya nemi hukumomi daban daban da su kara mai da hankulansu yayin da ake gab da fara gasar Olympic ta Beijing domin tabbatar da ganin an daidaita matsaloli cikin sauri ta hanyoyi masu amfani. (Sanusi Chen)