Darektan kula da ka'idoji na hukumar kare ikon mallakar ilmi ta kasar Sin, kuma kakakin hukumar Mr. Yin Xintian ya bayyana a gun wani taron manema labaru da aka shirya a cibiyar watsa labarai ta duniya da ke birnin Beijing a ran 29 ga wata cewa, kasar Sin za ta kare ikon mallakar ilmi na Olympics a tsanake.
Mr. Yin ya ce, gwamnatin kasar Sin ta kaddamar da ka'idojin kare alamun Olympics da kuma aiwatar da su, domin kare alamun Olympics, da tabbatar da halaliyar moriya ta mutanen da suke da ikon mallakar ilmi wajen samar da alamun Olympics, da kiyaye mutumcin gasar wasannin Olympics. Wadannan ka'idoji sun zama hakikanan matakai da kasar Sin ta dauka wajen kare ikon mallakar ilmi na Olympics.(Danladi)
|