Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-29 16:33:26    
Benin ta zama ta farko a tsakanin dukkan kungiyoyin kasashen waje wajen daga tuta a kauyen wasannin Olympics

cri
Ran 29 ga wata da safe, an yi bikin daga tutar kungiyar wakilan 'yan wasan kasar Benin a kauyen wasannin Olympic. Ta haka kungiyar wakilai ta Benin ta zama ta farko a tsakanin dukkan kungiyoyin wakilai na kasashen waje a fannin daga tuta a kauyen wasannin Olympic.

Chen Zhili, mataimakiyar shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing kuma shugaban kauyen wasannin Olympic na Beijing ta yi kyakkyawar maraba ga kungiyar wakilai ta Benin a gun bikin.

Charles Nobre, shugaban kungiyar wakilai ta Benin ya bayyana cewa, gasar wasannin Olympic ta Beijing wani kasaitaccen biki ne da 'yan Adam suke hada kansu. Benin ta aika da 'yan wasa 5 domin shiga gasar wasannin Olympic ta Beijing. Masukudinta shi ne amsa kirar ruhun wasannin Olympic, wato mai da hankali kan shiga gasanni.(Tasallah)