Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-29 16:21:19    
Nijeriya ta yaba wa aikin share fage na gasar wasannin Olympics ta Beijing

cri

A 'yan kwanakin baya a birnin Beijing, ministan da ke kula da harkokin cinikayya da wasannin Olympics a ofishin jakadancin kasar Nijeriya da ke a nan kasar Sin Mr. Ibrahim Isah ya bayyana cewa, hukumar gasar wasannin Olympics ta Beijing ta gudanar da aikin share fage da kyau, ya gamsu da filaye da dakunan wasanni musamman.

A yayin da yake zantawa da wakiliyarmu Tasallah, Mr. Isah ya fadi cewa, a 'yan kwanakin baya, ya taba kai ziyara a filaye da dakunan gasar wasannin Olympis da kuma kauyen Olympics, yana mamaki sosai kan filaye da dakunan da ke da inganci sosai, birnin Beijing ya samu babbar nasara wajen gina filaye da dakunan wasannin Olympics. Game da aikin tsaro na wasannin, Mr. Isah ya ce, a halin yanzu dai, dukkan al'umomin birnin Beijing suna kokari sosai domin cim ma burin gudanar da gasar wasannin Olympics cikin lumana.

Ban da wannan kuma, Mr. Isah ya yi bayani kan yadda 'yan wasa na kasar Nijeriya suke shirya gasar wasannin Olympics ta Beijing. Ya ce, kasar Nijeriya tana da kwarewa a Afirka a fannonin wasanni, a nan gaba ba da dadewa ba 'yan wasan kasar Nijeriya za su iso birnin Beijing. Ministan wasanni na kasar Nijeriya kuma zai halarci bikin bude gasar wasannin Olympics ta Beijing.(Danladi)