Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-29 16:20:23    
Tabas ne gasar wasannin Olympic ta Beijing za ta shiga tarihin dan Adam

cri
A ran 29 ga wata, Jaridar Lianhe Zaobao ta kasar Singapore ta bayar da labarin malam Yu Sui, furofesar a cibiyar nazari a kan duniyar yanzu na kasar Sin, kuma ta yi zaton cewa, tabas ne gasar wasannin Olympic na Beijing za ta yada ra'ayin wasannin Olympic, za ta bayar da kyakkyawan halin musamman da kasar Sin ke ciki, kuma za ta shiga tarihin wasannin motsa jiki na dan Adam sabo da nasara da ta cimma.

A cikin labarin, an ce, a kwanakin masu zuwa, za a fara yin gasar wasannin Olympic a karo na 29 a brinin Beijing tare da zaman lafiya, zumunta, da kuma ci gaba. Gwamnatin kasar Sin da jama'arta sun cika alkawarinsu, cikin shekaru 7 sun yi iyakancin kokarinsu wajen shirya gasar wasannin Olympic.

Labarin ya furta cewa, ko wace kasa dake shirya gasar wasannin Olympic tana son ta bayyana sifarta ga duk duniya, wannan ya zama karo na farko ne da kasar Sin ta shirya gasar wasannin Olympic, lokacin da ta nuna farin ciki, kasar Sin za ta dauki nauyin dake wuyanta, kuma ta yi iyakacin kokarinta don daidaita harkoki daban daban cikin nasara. (Zubairu)