Ran 29 ga wata a birnin Beijing, Mr. Gilbere Felli, darektan zartaswa mai kula da gasar wasannin Olympic na kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa ya bayyana cewa, matsayin ingancin iska na birnin Beijing ya fi matsayin da kasashen waje ke zato, yana tsammani cewa, akwai 'yar yiwuwar sauyawar lokacin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing domin ingancin iska.
A cikin mako da ya gabata, an yi hazo sosai a birnin Beijing. Bi da bi ne wasu kafofin watsa labaru na kasashen waje sun ba da bayani cewa, bayan yin amfani da matakan kayyade zirga-zirgar motoci a birnin Beijing, matsalar gurbatacciyar iska tana cigaba da tsananta. Game da wannan lamari, Mr Felli ya nuna cewa, ba a iya ganin ingancin iska ta hanyar duba da ido kawai, kamata ya yi a yi amfani da kididdigar kimiyya. Ya furta cewa, mutane da yawa suna tsammani cewa ingancin iska ba shi da kyau domin tsawon gani ya ragu. Amma muna gani cewa, wannan ba gurbatacciyar iska ba ne, hazo ne kawai.
Mr. Felli ya bayyana cewa, bisa halin yanzu ba a bukatar a kyara lokacin gasar wasannin Olympic. Amma ya nanata cewa, kwamitin gasar wasannin Olympic na kasa da kasa zai cigaba da mai da hankali kan ingancin iska na birnin Beijing, kuma zai tsai da shawara bisa kididdigar da aka samu.(Fatima)
|