A ran 29 ga wata da karfe 12 da minti 15 na tsakiyar rana, an kammala mika wutar gasar wasannin Olympic ta Beijing a birnin Shijiazhuang, wato hedkwatar lardin Hebei.
An fara bikin mika wutar gasar wasannin Olympic a filin dakin tunawa ta Xibaipo. Tsawon hanyar mika wutar a birnin Shijiazhuang ya kai kilomita 9.3, kuma masu mika wutar su 188 sun shiga aikin mika wutar.
Daga ran 29 zuwa 31 ga watan Yuli, za a mika wutar gasar Olympic a birane Shijiazhuang, Qinhuangdao da Tangshan na lardin Hebei.(Asabe)
|