Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-29 15:54:08    
Jaridar People Daily ta bayar da labarin cewa, hasashe iri uku wato taron wasannin Olympic cikin kyakkyawan yanayi, da taron wasannin Olympic da aka yi ta hanyar kimiyya da fasaha da kuma taron wasannin Olympic dake dacewa da al'adun 'yan adam su ne Gasar Olympic na Beijing

cri
Bayan kwanaki 10, za a soma gasar Olympic na Beijing. A ran 29 ga watan, jaridar People Daily ta bayar da wata labarin cewa, hasashe iri uku wato taron wasannin Olympic cikin kyakkyawan yanayi, da taron wasannin Olympic da aka yi ta hanyar kimiyya da fasaha da kuma taron wasannin Olympic dake dacewa da al'adun 'yan adam su ne Gasar Olympic na Beijing.

Labarin ya ce, hasashe iri uku nan da hasashen gasar Olympic wato "zaman lafiya, zumunci, da bunkasuwa" ra'ayinsu iri daya ne, wannan ya amsa kiran bunkasuwar zamanin yanzu.

Bugu da kari, labarin jarida ta ce, a bisa zaben da aka yi a hankali sosai don samun bunkasuwa a cikin shekaru 30 da suka gabata, wato bayan da kasar Sin ta fara yin gyare gyare a gida da bude kofa ga duniya har zuwa yanzu, kuma sabo da babban sakamakon kasar Sin ta samu wajen zamanintar da kasa, an gabatar da hasashen nan iri uku. A karkashin jagorancin hasashen nan, a cikin shekaru 7 na shirya gasar Olympic, jama'ar kasar sun sami moriya da yawa, zaman jama'ar kasar ya canja sosai.

Dadin dadawa, labarin nan ya ce, a duk tsawon lokacin da aka zamanintar da kasar Sin, hasashe iri uku da aka gabatar a gasar Olympic ta Beijing sun kafa buri mai kyau na dacewa da al'adun 'yan adam, kuma hasashen irin uku sun samar da karfin ingiza na ruhun dake daga duk fanoni, cikin daidaituwa da kuma iya samun bunkasuwa mai dorewa ga bunkasuwar zaman al'umma. Shi ne dalilin da ya sa mambobin kwamitin wasannin Olympic na duniya suka zabi birnin Beijing kafin shekaru 7, kuma sun yi imani da cewa, "wannan babban abu ne da za a yi gasar Olympic a kasar da yawan mutanenta ya kai kashi 20 a cikin kashi dari a duniya." (Asabe)