Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-29 10:56:14    
An fara mika wutar yola ta gasar wasannin Olympic ta Beijing a birnin Shijiazhuang na lardin Hebei

cri

Ran 29 ga wata an fara mika wutar yola ta gasar wasannin Olympic ta Beijing a lardin Hebei da ke tsakiyar kasar Sin har na kwanaki 3, ran nan an mika wutar yola ta gasar wasannin Olympic ta Beijing a birnin Shijiazhuang, hedkwatar lardin Hebei.

Da misalin karfe 8 na safe, anka fara bikin mika wutar yola ta gasar wasannin Olympic ta Beijing a filin dakin tunawa ta Xibaipo na birnin Shijiazhuang. Kuma mai daukan wutar na 21 ya fara mika wutar yola ta gasar wasannin Olympic ta Beijing a cikin unguwoyin birnin Shijiazhuang, gaba daya tsawon hanyar mika wutar ya kai kilomita 9.3 a cikin birnin, kuma masu rike wuta su 188 sun halarci wannan bikin mika wuta, da karshe za su isa dakin motsa jiki na lardin Hebei.

Tun daga ran 29 zuwa ran 31 ga watan Yuli, za a mika wutar yola ta gasar wasannin Olympic ta Beijing a birane guda 3 na lardin Hebei, wato biranen Shijiazhuang da Qinhuangdao da Tangshan.(Fatima)