Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-28 21:06:59    
Birnin Beijing ya shirya sosai wajen ba da hidimar kudi ga baki a yayin da ake shirya gasar wasannin Olympics ta Beijing

cri

A ran 28 ga wata a cibiyar watsa labarai ta duniya a shekarar 2008 da ke birnin Beijing, mataimakin shugaban kungiyar bankuna na kasar Sin Mr. Yang Zaiping ya bayyana cewa, a halin yanzu dai, birnin Beijing ya shirya sosai wajen ba da hidimar kudi mai kyau ga 'yan wasanni, da manema labaru, da masu yawon shakatawa da suka zo daga kasashen waje a yayin da ake shirya gasar wasannin Olympics ta Beijing.

Mr. Yang ya gabatar da cewa, a halin yanzu dai, kashi 85 daga cikin dari na bankunan kasuwanci na yankin Beijing suna iya bayar da babbar hidimar kudi ta jama'a ga baki ciki har da musanyar kudin waje da cakin kudi, haka kuma suna bayyana alamun musanyar kudi da kuma farashin kudin da Sinanci tare da Turanci. Haka kuma tashoshi 82 na bakuna suna iya bayar da hidimar musanyar kudi a cikin duk awoyi 24. Yawancin na'urorin taimakon kansa na banki wato ATM suna kula da harkoki da katin VISA, da kuma Master Card da dai sauransu.(Danladi)