Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-28 20:54:05    
Hukumar kasuwanci ta birnin Beijing ba ta dakatar da bayar da takardar sanarwa game da neman visa na shigo kasar Sin kan ayyukan kasuwanci ba

cri
A ranar 28 ga wata, a lokacin da wani jam'in hukumar kasuwanci ta Beijing ke zantawa da manema labaru, ya bayyana cewa, hukumar ba ta taba dakatar da bayar da takardar sanarwa ga baki daga kasashen ketare da su samu visa na shigo kasar Sin don ayyukan kasuwanci ba.

Akwai labari daga wani kamfanin dillancin labaru na waje na cewa, 'hukumar kasuwanci ta birnin Beijing ta riga ta dakatar da bayar da takardar sanarwa ga mutanen kasashen waje da ke neman visa don ayyukan kasuwanci a nan kasar Sin.' Wannan jami'in ya ba da wannan amsa ne kan maganar, inda ya ce, tun daga watan Yuli, hukumar kasuwanci ta birnin Beijing ta kan bayar da takardun sanarwa kamar 150 a kowace rana, wato ya karu da kashi 52 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara. (Bilkisu)