Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-28 16:19:42    
An shirya nune-nune na al'adu da wasannin motsa jiki a dukkan dakunan gasar wasannin Olympic na Beijing

cri
A cikin wa'adin shirya gasar wasannin Olympic na Beijing, yan kallo za su iya jin dadin nune-nune na al'adu da wasannin motsa jiki da aka shirya lokacin da suke kallon gasar wasannin Olympic.

A ran 28 ga wata, ministan harkokin al'adu na kwamitin shirya gasar wasannin Olympic na Beijing Mr. Zhao Dongming ya bayyana cewa, lokacin da ake shirya gasar wasannin Olympic na Beijing, za a shirya wasannin Kongfu, da wasannin kankwashe jiki, da rawa, da dai sauransu a dakunan gasar wasannin Olympic.

Kazalika kuma, Mr. Zhao Dongmin ya bayyana cewa, ban da wasannin kwaikwayo da aka shirya a cikin dakunan, za a kafa filin al'adu guda 24 a birnin Beijing, don shirya aikace-aikacen al'adu irin daban daban.

Ban da wannan kuma, za a shirya bikin nune-nune na duniya sama da dari hudu a cikin birnin Beijing, da sauran birane. (Zubairu)