
A 28 ga wata, an mika wutar gasar wasannin Olympic a birnin Anyang na lardin Henan, birnin ne dake da dogon tarihi da al'adum, kuma wurin asalin rubutun Sinanci da aka sassaka a kan kashi ko kokon bayan kunkuru.

Birnin Anyang ya zama zango na hudu ne lokacin da aka mika wutar gasar wasannin Olympic na Beijing. An fara mika wutar a karfe 8 da minti 8 na safe a hukunce.

Tsawon hanyar mika wutar a zangon birnin Anyang ya kai kilomita 5.91, kuma akwai masu mika wutar guda 208 da suka shiga aikin mika wutar. (Zubairu)
|