Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-25 17:06:38    
An kafa tawagar 'yan wasa ta gasar wasannin Olympics ta kasar Sin a hukunce

cri

Yau a birnin Beijing, an kira taron kafa tawagar 'yan wasa ta kasar Sin da za ta halarci gasar wasannin Olympic ta Beijing. Madam Liu Yandong, mambar majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta halarci wannan taro.

Tawagar 'yan wasa ta kasar Sin ta hada da mutane 1099, a ciki da akwai 'yan wasa 639 wadanda za su halarci mayan ayyukan wasanni iri iri har 28 na gasar wasannin Olympic gaba daya. Kuma wannan karo na 4 ne a jere da Guo Jingjing, yar wasan iyo, da Tan Zongliang, dan wasan harbi, da Li Nan, dan wasan kwallon kwando, suka halarci gasar wasannin Olympic. Dadin dadawa kuma, 'yan wasa 469 ne za su halarci gasar a karo na farko.

Mr. Liu Peng, shugaban tawagar 'yan wasan kasar Sin kuma shugaban hukumar wasannin motsa jiki ta kasar ya bayyana cewa, sassan wasannin motsa jiki na kasar Sin sun riga sun share fage ga gasar wasannin Olympic ta Beijing har na tsawon shekaru da dama, ba shakka 'yan wasan za su yi namijin kokari a duk fannoni. A sa'i daya, Mr Liu ya jaddada cewa, tawagar kasar Sin za ta dauki matsayin da ta dade tana tsayawa wajen yaki da shan kwayoyi masu kara kuzari a cikin wasanni.(Fatima)