Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-25 16:51:08    
An riga an shirya sosai wajen bude kauyen gasar wasannin Olympics ta Beijing

cri

Kakakin kauyen gasar wasannin Olympics ta Beijing Madam Deng Yaping ta bayyana a ran 25 ga wata a birnin Beijing cewa, za a bude kauyen gasar a ran 27 ga wata a hukunce, a halin yanzu dai, an riga an shirya sosai wajen bude kauyen gasar wasannin Olympics ta Beijing.

Kauyen gasar wasannin Olympics ya zama wurin kwana na 'yan wasanni da ke halartar gasar wasannin Olympics da kuma jami'ai da ke raka su. Madam Deng ta ce, ban da na'urorin kasuwanci kamar bankuna da kantuna, kauyen gasar wasannin Olympics ta Beijing ya kaddamar da dakunan internet da cibiyoyin kayayyakin fasahar jama'a. Wajen samar da abinci mai inganci kuma, kauyen Olympics zai sa ido a duk yunkurin samar da abinci, domin tabbtar da samar da abinci mai inganci ga 'yan wasanni da jami'ai. Ban da wannan kuma, cibiyar ba da hidimar addinai ta kauyen Olympics za ta kebe yankuna yin salla ga manyan addinai biyar wato Kiristoci, da Buddah, da Musulunci, da Judaism, da kuma Hindu, tare da na'urorin da abin ya shafa ga sauran addinai, domin jama'ar da ke bin addinai daban daban su yi zaman jituwa tare.(Danladi)