
An kammala zagayawa da fitilar wasannin Olympics ta Beijing yau Asabar a birnin Dalian na lardin Liaoning dake arewa maso gabashin kasar Sin.

Birnin Dalian, zango na karshe ne, inda aka yi yawo da fitilar wasannin. Wata tsohuwar shahararriyar 'yar wasa wato zakarar wasan guje-guje da tsalle-tsalle na wasannin Olympics ta zama ta farko daga cikin mutane 208 masu daukar wutar wasannin.

An kuma labarta cewa, za a kai wutar wasannin zuwa lardin Shandong domin ci gaba da yawo da ita. ( Sani Wang )
|