Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-18 20:59:49    
Jacques Rogge na sa san alheri kan ingancin iskar Beijing a lokacin wasannin Olympics

cri
Kwanan baya, a lokacin da ya ke zantawa da manema labaru na kasar Faransa, Mr. Jacques Rogge, shugaban kwamitin wasannin Olympics na Beijing ya bayyana cewa, yana sa ran alheri ga ingancin iskar Beijing a lokacin wasannin Olympics, kuma ya yi babban yabo ga matakai a jere da Beijing ta dauka a kwanan baya, don kyautata muhalli.

Kamfanin dillancin labaru na AFP na kasar Faransa ya bayar da labari a ranar 18 ga wata cewa, Mr. Rogge ya ce, kullum hukumomin da abin ya shafa na kasar Sin suna yin kokari don kyautata muhalli. An zartas da sabbin dokokin shari'a da ke da nasaba da kiyaye muhalli, kuma sun dauke masana'antun da ke gurbata muhalli da ke nan birnin Beijing zuwa wasu wurare, yayin da suke kokarin dasa itatuwa bisa babban mataki a wasu lalatattun wuraren da ke da kananan duwatsu, bugu da kali kuma an kyautata tsarin tsabtace ruwa, da kuma saukaka zirga-zirgar motoci, da dai sauransu, ba kawai wadannan matakai su ba da tabbaci wajen ingancin iskar Beijing a lokacin wasannin Olympics ba, har ma a hakika dai za su warware matsalolin muhalli mai dorewa. (Bilkisu)