
Ran 18 ga wata a nan birnin Beijing, Madam Yan Jiangying kakaki ta hukumar sa ido kan magani da abinci ta kasar Sin ta nuna cewa, kasar Sin tana sa ido na musamman kan ingancin magani da abincin da suka shiga kauyen wasannin Olympics da filayen wasannin Olympics. Yanzu dukkan magani da abincin da aka bincke sun kai matsayin cancanta.

A gun taron manema labarun da aka yi a wannan rana, Madam Yan Jiangying ta bayyana cewa, kwamitin shirya wasannin Olympics na Beijing da hukumomin da abin ya shafa sun shirya isasshen magani ,da kayayyakin aikin likita, da mutane masu aikin likita, da kudi, ta haka domin tabbatar da samar da isasshen ingantaccen magani ga 'yan wasa, da 'yan kallo, da kuma jama'a yayin da ake gudanar da wasannin Olympics.
|