Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-09 17:56:37    
Ya zuwa yanzu an fitar da lambobin zinariya 4 a gun gasar Olympic ta Beijing a yini na farko

cri

A ran 9 ga wata, wato yini na farko na gasar Olympic ta Beijing, a gun gasannin karshe na harbe-harbe na maza da mata masu zango mita 10 da gasar daga nauyi ta mata, da gasar tseren keke ta maza da aka yi a kan hanyar mota, an fitar da lambobin zinariya 4.

A gun gasar harbe-harbe ta mata, 'yar wasa ta kasar Czech Katerina Emmons ta samu lambar zinariya, ta kuma yanke matsayin bajinta na wannan gasa.

A waje daya kuma, a gun gasar daga nauyi ta mata da 'yan mata da nauyinsu bai wuce kilogram 48 ba suke halarta, 'yar wasa ta kasar Sin Chen Xiexia, mai shekaru 25 da haihuwa ta samu lambar zinariya da maki kilogram 212. Ta kuma yanke matsayin bajinta na gasar Olympic. Wannan kuma lambar zinariya ta farko da kungiyar wakilan 'yan wasa ta kasar Sin ta samu a gun wannan gasar Olympic.

Sannan kuma, a gun gasar harbe-harbe ta maza mai zango mita 10 da aka yi a ran 9 ga wata da yamma, dan wasa na kasar Sin Pang Wei ya kuma samu wata lambar zinariya.

A ran 9 ga wata, a gun gasar tseren keke ta maza ta wasannin Olympic ta Beijing da aka yi a kan hanyar mota, Samuel Sanchez, wani dan wasa na kasar Spain ya samu lambar zinariya. (Sanusi Chen)