
Ran 18 ga wata, jaridar "people's daily" ta kasar Sin ta bayar da bayanin edita cewa, an gudana da taron wasannin Olympics na Beijing ta hanyar tsimi ya zama wani abin kyalkyali.
An bayyana cewa, a cikin shekaru 7 da suka wuce yayin da Beijing yana shirya wasannin Olympics, kullum yana tsayawa kan tsarin gudanar da wasannin Olympics ta hanyar tsimi. A cikin sababbin filayen wasannin da aka gina, an yi amfani da fasahohin kiyaye muhalli, wannan ya tsimi kudi da makamashi. Ban da haka kuma, yayin da ake gyara gine-gine na birnin Beijing, an yi amfani da sababbin fasahohi da yawa. Abin da brinin Beijing ya yi ya sami yabawa daga fannoni dabam daban na kasa da kasa, kuma ya sami goyon baya daga jama'a sosai.

Wannan bayanin edita ya bayyana cewa, gudanar da wasannin Olympics ta hanyar tsimi ya dace da tunanin "wasannin Olympics dake da muhalli mai kyau, da wasannin Olympics mai kimiyya da fasaha, da wasannin Olympics mai al'adu". Ya ce, dole ne a cigaba da darajanta karfin jama'a, da kudi da kayayyaki domin gudanar da wani ingantaccen wasannin Olympics na Beijing ta hanyar tsimi.
|