Ni'imtaccen wurin al'ajabi na dutsen Tianshan

cri 2011-09-22 18:09:53

Ranar yau, mun tashi daga garin Kuqa zuwa birnin Kashgar. Ashe, hanya ce mai tazara sosai domin mun kwashe awa kusan bakwai a kan hanya kafin mu isa jihar Xinjiang wanda ta kasance daya daga cikin jihohin kasar Sin dake da dogon tarihi da kuma al'adu iri daban daban inda kabilun kasar ke zama tare cikin jituwa, na kuma lura cewa jihar tana da da girma. Domin na ji an ce, fadinta ya ninka kusan sau biyu na kasarmu Najeriya. A hakika dai, kasar Sin babbar kasa ce.

1 2 3
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China