Ni'imtaccen wurin al'ajabi na dutsen Tianshan

cri 2011-09-22 18:09:53

A yayin ziyararmu ta ranar yaji, lokacin da muke cikin garin Kuqa, mun samu zuwa wani ni'imtaccen wurin yawon bude ido dake dutsen Tianshan. Mun samu damar ganin abubuwan al'ajabi da yawa a wannan wurin, kamar su, karamin kogin karkashin kasa da har yanzu ba'a da masaniya kan tushensa ko asalinsa ba, ruwa na fitowa daga kasa, kuma ruwa na malala har karkashin kasa kafinsu shiga a wani wuri nan da nan. Bugu da kari, a cikin wannan kwazazzabo , akwai wasu duwatsun da surorinsu ke kama da dabbobi iri iri. A hakika dai, wannan wuri ya ba mu mamaki kwarai. Wani ma'aikacin dake aiki a wannan wuri ya gaya mana cewa, wannan ne karo na farko da 'yan Najeriya suka kawo ziyara. A gaskiya jin haka, ya sani nuna farin ciki kwarai. A nan gaba, idan wata damar ta samu ina sake kawo ziyara.
1 2 3
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China