logo

HAUSA

WHO: Yawan mutanen da suka harbu da cutar COVID-19 ya karu da kashi 71% a makon da ya wuce

2022-01-07 14:00:15 CMG

WHO: Yawan mutanen da suka harbu da cutar COVID-19 ya karu da kashi 71% a makon da ya wuce_fororder_B2

Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta sanar a jiya Alhamis cewa, daga ranar 27 ga watan Disamban bara zuwa ranar 2 ga watan da muke ciki, yawan mutanen da suka harbu da cutar COVID-19 a kasashe daban daban, ya karu da kaso 71%, idan an kwatanta da makon da ya gabace shi, inda jimillar ta kai kimanin mutum miliyan 9 da dubu dari 5. Sa’an nan sabbin wadanda suka rasa rayuka sakamakon cutar, sun ragu da kaso 10%.

WHO ta ce, sabbin masu kamuwa da cutar COVID-19 sun karu a yankuna daban daban. Kana an samu karuwa mai girma a nahiyar Amurka, wadda ta kai kaso 100 cikin dari bisa adadin makon da ya gabata. Sauran yankunan da suka fi fama da karuwar sabbin masu kamuwa da cutar sun hada da yankin kudu maso gabashin Asiya, da na Turai, inda karuwar da aka samu a wuraren ta kai kashi 78% da 65%.

Kaza lika idan an yi la’akari da yawan mutanen da suka kamu da cutar a cikin yawan al’umma, jimillar ta fi yawa a nahiyar Turai. Yayin da kasashen da suka samu mafi yawan sabbin masu kamuwa da cutar a makon da ya wuce, su ne Amurka, da Birtaniya, da Faransa, da Sifaniya, da kuma kasar ta Italiya. (Bello Wang)

Bello