logo

HAUSA

Duba Baya 2021: Cutar Korona Da Kalubaloli a Nijeriya Da Afirka

2021-12-24 13:39:46 CMG

Duba Baya 2021: Cutar Korona Da Kalubaloli a Nijeriya Da Afirka_fororder_2021-1

Abubuwa da dama sun faru a shekarar da ke zuwa karshe wato 2021, a ciki ma har da ci gaba da yaki da cutar korona (Covid-19) da fafutukar kawar da ita da kuma samun allurar rigakafinta (vaccine) musamman ma a kasashen nahiyar Afrika. Kidayar hukumar lafiya ta duniya WHO a farkon makon watan Disamba na 2021 dai ya nuna kimanin mutane miliyan 8.8 ne suka kamu da cutar a Afirka tare da kuma sama da 217,000 da suka rasa rayukansu.

A Nijeriya kuma, tun farkon bullowar cutar Covid-19 a Nijeriya a shekarar 2020, ya zuwa ranar 22 ga wata, kimanin mutane 231413 ne suka kamu da ita da kuma wadanda ta hallaka misali 2,991 kamar yadda cibiyar kare cututtuka NCDC ta bayyana a farkon makon watan Disamban bana.

Jami’an gwamnatin Nijeriya dai suna iyakacin kokarinsu don shawo kan wannan cuta a yayin da aka dauki matakai daban-daban na kariya da kiyayewa. Amma kamar sauran kasashe masu tasowa, Nijeriya tana fuskantar kalubale na karancin allurar rigakafi wato (vaccine). Kamar yadda muka sani ita dai wannan allurar ba a hada ta a Nijeriya, amma a yanzu haka kasar ta dogara ga tallafin kungiyar raba rigakafin (COVAX) mai goyon bayan hukumar lafiya ta duniya (WHO). Gwamnatin tarayya ma na kokarin sa kudi don sayo allurar daga kasashen ketare.

Duba Baya 2021: Cutar Korona Da Kalubaloli a Nijeriya Da Afirka_fororder_2021-2

Tun farko dai kasar Sin ta dukufa da taimaka ma Nijeriya da kayayyakin kandagarkin cutar Covid-19 da jami’an kiwon lafiya da likitoci, da kayan aiki. Jami’an gwamnati daga Sin da Nijeriya kuma suna cikin tattaunawa wajen ganin allurar rigakafi irin na kasar Sin wato SinoVac and SinoPharm sun shiga ayarin alluran da ake amfani da su yanzu haka a Nijeriya.

Tabbas, sauran kasashen nahiyar Afirka na fama da kalubalen karancin allurar rigakafin, a halin da ake ciki dai yanzu kimanin kashi 8% ne kawai suka samu damar yin allurar rigakafin Korona (Covid-19 vaccine) a duk fadin Afirka wacce ke da mutane sama da biliyan 1.3. A nan ma, kasar Sin ta taka rawar gani a inda ta kai allurar rigakafin irin ta SinoVac da ta SinoPharm a kasashe da dama a karkashin kungiyar taimako ta kasar wato (China Aid).

A farkon shekarar nan ne ma a watan Janairu ministan harkokin wajen kasar Sin, wato Wang Yi ya ziyarci kasashe biyar a Afirka a inda ya jaddada kudirin kasar Sin na hada kai da kasashen Afirka domin yaki da cutar da kuma samun mafita ta hanyar taimakawa da allurar rigakafin da kuma fuskantar kalubalen matsalolin da cutar ta haifar wato durkushewar tattalin arzikin kasashe da yawa a nahiyar da matsalolin dakushewar cinikayya. Ita dai wannan ziyara ta minista Wang Yi ta samo tushe ne tun shekaru sama da talatin da suka gabata a yayin da duk farkon shekara sai ministan harkokin wajen kasar Sin ya kai ziyara a nahiyar Afirka. Wannan dai wani abu ne mai muhimmanci tsakanin kasar Sin da kasahen Afrika wanda kuma yake kara dankon zumunta.

A cikin watan Agusta, shugaba Xi Jinping na kasar Sin a sakon sa da ya tura a wani taro na kasa da kasa da hadin gwiwa, ya yi alkawarin baiwa kasashe marasa karfi gudumawar allurar rigakafin biliyan 2 da kuma kudade dalar Amurka miliyan 100 don karfafa kungiyar rabo ta COVAX mai goyon bayan hukumar lafiya ta duniya WHO. Hakazalika, a taron ministoci na 8 na dandalin FOCAC wanda aka yi a garin Dakar na kasar Senegal a karshen watan Nuwamba, shugaba Xi a cikin jawabinsa ga taron ya bayyana cewa hadin gwiwar kasar Sin da Afrika hadin gwiwa ne mai dogon zamani da kuma amfani ga juna. A cikin jawabi nasa ya kara jaddada bada gudumawar allurar rigakafi biliyan 1 ma kasashen Afrika.

A Afrika dai rashin allurar rigakafin (vaccine), babban kalubale ne, abin da kuma ya haddasa wannan kalubale shi ne rashin cibiyar hada allurar da rashin isassun kudade. Amma wasu kasashe kamar Egypt suna kokarin ganin sun samu damar dasa cibiyar hada allurar rigakafin a kasashensu tare da hadin gwiwar kasar Sin.

Hakazalika, ina matukar fatan cewa duk da kalubalen da ake fuskanta a kasashenmu, bada dadewa ba za’a fita daga matsalolin wannan annobar ta Covid-19 a Nijeriya da Afirka da ma duniya baki daya. Afirka da kasashen dake cikinta sun saba da fama da irin wadannan matsalolin kuma suna fita a ko da yaushe. Fita daga matsalar Covid-19 dai ba yakin kasa daya ba ne, yaki ne wanda ya kamata kasashe za su taimakawa juna da hadin gwiwa domin cin nasara. Kasar Sin kamar yadda aka sani ta taka rawar gani sosai wurin irin wannan taimakon da hadin gwiwa domin dakile cutar ta Covid-19.( Lawal Sale )

Lawal Sale