logo

HAUSA

Har Yanzu Akwai “Sauran Rina A Kaba” Game Da Dakile Annobar COVID-19 A Duniya

2021-12-23 17:16:10 CRI

Har Yanzu Akwai “Sauran Rina A Kaba” Game Da Dakile Annobar COVID-19 A Duniya_fororder_covid

Kusan a iya cewa ba wani kalubalen da duniya ta sha fama da shi a ’yan shekarun baya bayan nan, da tasirinsa ya wuce na bazuwar annobar numfashi ta COVID-19, wadda bayan bullarta shekaru 3 da suka gabata, masana suka dukufa wajen nazarin dabarun dakile ta, kama daga lalubo fasahohin kandagarki, da na hana ci gaba da bazuwarta, zuwa samar da alluran rigakafin cutar a matakai daban daban.

A mataki na samar da rigakafi, kamfanonin harhada magunguna da dama sun dukufa, wajen kirkiro rigakafin cutar domin amfanin bil adama, kuma tuni aka yiwa al’ummun duniya daban daban rigakafin, musamman ma a kasashe masu wadata, ko da yake an bar wasu sassan kasashe matalauta a baya a wannan fanni.

Wani abun lura game da yaduwar wannan annoba shi ne, yadda take kara sauya nau’o’i, ko da yake masana da dama na hasashen sauyin ba zai hana alluran rigakafin da ake yiwa al’umma amfani a jikin su ba. Duk da haka, ana iya cewa abun damuwa ne, ganin yadda ya zuwa shekarar nan ta 2021, COVID-19 ta yi ajalin mutane sama da miliyan 3, adadin da ya haura jimillar wadanda cuta mai karya garkuwar jiki, da zazzabin cizon sauro, da tarin fuka suka hallaka a shekarar 2020, kamar dai yadda hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO ta bayyana.

Masana a fannin yaki da wannan cuta ta COVID-19 na alakanta ci gaba da mamayar da annobar ke yi, da rashin daidaito wajen samar da rigakafin a tsakanin sassan duniya, inda da dama ke ganin duk da nasarar da fannin kimiyya ya samu na bullo da rigakafin annobar cikin gaggawa, a hannu guda kuma, tsarin raba su ga al’ummun duniya bisa daidaito, na zama kadangaren bakin tulu ga yakin da ake yi da cutar.

A cewar WHO, kusan mutane dubu 50 ne ke rasuwa a duk mako a  duniya sanadiyyar harbuwa da wannan cuta. Kuma yayin da wasu kasashe musamman masu wadata ke yiwa al’ummun su rigakafin karfafa garkuwar jiki, rabin kasashe mambobin hukumar ta WHO ne kadai suka iya kaiwa ga yiwa kaso 40 bisa dari na al’ummun su rigakafin a bana, saboda rashin samun isassun alluran yadda ake bukata.

Idan mun kalli wadannan alkaluma da kyau, za mu iya gane cewa, lallai akwai sauran rina a kaba game da bukatar da ake da ita ta cimma nasarar yiwa kaso mai tsoka na al’ummun duniya rigakafin COVID-19 cikin gaggawa. Kuma kamata ya yi kasashe masu wadata su sauya salon raba rigakafin da suke aiwatarwa a hanlin yanzu, su kauracewa boye rarar rigakafin da suke samarwa a cikin gida, tare da kara ba da gudummawa ga shirin nan na COVAX na daidaita samar da rigakafin ga sassan duniya, ta yadda “za a guda tare a kuma tsira tare”. (Saminu Alhassan)