Yawan sabbin masu kamuwa da cutar COVID-19 a rana guda ya karu sosai a Canada
2021-12-21 15:31:40 CRI
Gidan telibijin na kasar Canada ya ruwaito cewa, a ranar 20 ga wata, karo na farko ne yawan sabbin masu kamuwa da cutar COVID-19 a rana guda ya wuce dubu 10, ya kai 10621, yayin da yawan masu kamuwa da cutar ya kai 1894981 baki daya a kasar.