logo

HAUSA

Me ya sa dangantakar Sin da Rasha ke dada inganta?

2021-12-16 18:56:46 CRI

Me ya sa dangantakar Sin da Rasha ke dada inganta?_fororder_1

Jiya Laraba shugabannin kasashen Sin da Rasha sun gana ta kafar bidiyo, inda shugaba Xi ya bayyana fatansa na haduwa da Putin a yayin gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu a Beijing, shi ma Putin na Rasha ya ce yana matukar fatan ziyartar kasar Sin cikin hanzari tare da halartar bikin bude gasar wasannin Olympics din. A yayin ganawarsu wannan karo, shugabannin biyu sun yi musanyar ra’ayoyi kan batutuwa da dama da suka kunshi huldodi, da hadin-gwiwarsu. Kuma alkawarin da suka yiwa juna, wato haduwa da juna a yayin gasar Olympics, ya shaida dadadden zumunci da kuma fahimtar juna ta fannin siyasa a tsakanin kasashen biyu.

Me ya sa dangantakar Sin da Rasha ke dada inganta?_fororder_2

Ganawar ita ce karo na biyu da shugabannin biyu suka yi ta kafar bidiyo tun shiga shekarar da muke ciki, kana karo na 37 ke nan tun shekara ta 2013. Ba safai a kan ga irin wadannan shawarwarin da aka sha yi tsakanin shugabannin kasa da kasa ba, sai shugabannin Sin da Rasha. A halin yanzu dangantakar Sin da Rasha na cikin lokaci mafi kyau a tarihi, inda ake samun manyan nasarori a bangarorin hadin-gwiwarsu.

Nan da wata guda ko fiye mai zuwa, shugaba Xi da shugaba Putin za su gana ido da ido karo na farko tun barkewar annobar COVID-19, inda za su sanya hannu kan wasu muhimman takardun hadin-gwiwa, don sa kaimi ga ci gaban dangantakarsu. Hadin-gwiwar kasashen biyu ba samar da alheri ga al’ummominsu kawai za ta yi ba, har ma za ta taimakawa zaman lafiya da ci gaban duniya baki daya. (Murtala Zhang)