logo

HAUSA

Sin: Amurka na yin amfani da batun Xinjiang wajen hana ci gaban kasar Sin

2021-12-14 09:59:26 CMG

Sin: Amurka na yin amfani da batun Xinjiang wajen hana ci gaban kasar Sin_fororder_1214-Xinjiang-bello-2

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a jiya Litinin cewa, kasar Amurka ta yarda da karairayin da ake yadawa a duniya, dangane da jihar Xinjiang ta kasar Sin, inda ta sake sanya takunkumi kan wasu mutane da hukumomi na kasar Sin, bisa dalilin wai kare hakkin dan Adam a jihar Xinjiang ta kasar Sin.

A cewar Wang, matakin da kasar Amurka ta dauka ya zama tsoma baki cikin harkokin gidan kasar Sin, da keta ka’idojin kasa da kasa, da illata huldar dake tsakanin Sin da Amurka. Saboda haka kasar Sin ta ki yarda da matakin, ta kuma yi Allah wadai da shi da babbar murya.

Jami’in ya kara da cewa, batun Xinjiang yana cikin harkokin cikin gida na kasar Sin, kana al’ummun duniya sun ganewa idanunsu yadda ake samun ci gaban tattalin arzikin cikin matukar sauri a jihar, inda manufofin kasar Sin dangane da jihar Xinjiang ke samun karbuwa sosai tsakanin al’ummun kasar. Kasar Amurka sam ba ta da ikon tsoma baki cikin harkokin gidan kasar Sin, in ji jami’in. (Bello Wang)

Bello